9 Nuwamba 2021 - 16:15
​Afghanistan: AN Fara Yi Wa Yara Riga Kafin Cutar Shan Inna A yau Litini

A yau litinin ce MDD tare da hadin guiwa da hukuma mai kula da yara ta majalisar, wato UNICEF suka fara yi wa yara ‘yan kasa da shekaru 5 riga kafin cutar shan Inna ko Polio a duk fadin kasar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa MDD ta fara wannan aikin ne tare da amincewar gwamnatin Taliban, kuma aiki zai dauki kwanaki hudu cur ana gudanar da shi a duk fadin kasar. Har’ila yau ana saran za'a yi wa yara kimani miliyon 10 ‘yan kasa da sheru 5 a duniya a kasar a cikin wadannan kwanaki.

Ministan kiwon lafiya na gwamnatin rikon kwarya ta Taliban Dr Qalandar Ebad ya bayyana cewa cutar Shan Inna bala’ii ve ga yara wacce idan ba’a tare ta ba to zata kashe yara ko ta illatasu a duk tsawon rasyuwarsu.

A halin yanzu dai kasashen Afganistan da Pakista ne kawai suke rage basu kawo karshen cutar a duniya ba. Kuma wannan ba zai rasa nasa ba mamayar da Amurka da kasashen yamma suka yi wa kasar ta Afanistan na tsawon shekaru 20 ba. Wanda ya hana zaman lafiyar da zai bawa MDD damar aiki a wannan bangaren.

342/